How to track a lost phone?
GABATARWA (Introduction)
Rasa waya a wannan zamanin tamkar rasa zuciya ce, musamman idan tana ɗauke da muhimman bayanai kamar WhatsApp, Google account, hotuna, kudade na banking apps, da sauran muhimman bayanai. A darasin mu na yau zan rubuta hanyoyin da ake bi wajen gano wayar da ta ɓace ko aka sace. Zamu yi bayani sosai yadda kowa zai fahimta. Waɗannan hanyoyi zasu taimaka maka ka san inda wayarka take, ko an kashe ta, ko kuma an cire SIM ɗinka.
VIDEO: Yadda zaka samu 1k YouTube Subscribers A Kullum
Cikakken Bayani da Mataka
Mataki na 1️⃣. Yi amfani da apps mai suna Find My Device (Android) idan baka dashi, ka shiga Play Store kayi download
Idan kana amfani da Android (Samsung, Tecno, Infinix, Xiaomi, Pixel da sauransu), Google Find My Device shi ne hanya mafi sauƙi wajan gano wayar da ta ɓace.
Matakai:
- Ka samu wata wayar sai kayi logging na e-mail ɗinka, sai ka bude browser: Chrome, Opera, Edge.
- Ka rubuta: Find My Device
- Ka shiga da Google account ɗin da ke cikin wayar da taɓace.
- Idan wayar tana kunne kuma ana amfani da Internet, zaka ga accurate location ɗinta.
VIDEO: Yadda zaka kulle ATM da ya ɓace ko aka sace
✅Abubuwan da zaka iya yiwa wayar ta hanyar amfani da -find my device - App koda bata kusa da kai👇👇
- Play sound- zata yi ƙara ko da tana silent. Hakan zai taimaka idan wayar tana kusa zaka ji ƙarar ta.
-Secure device- zaka iya kulle wayar gaba ɗaya, hakan zai hana wanda ya saci wayar ɗaukar Bayanan ka ko kuma satar maka kuɗi.
- Erase device- zaka iya goge dukkan bayanai idan kana tsoron kada a sace su.
MATAKI NA 2️⃣. Amfani da Find My iPhone (iPhone Users)
Ga masu iPhone kuma:
- Je zuwa: https://www.icloud.com/find
- Shiga da Apple ID naka.
- Za ka ga location ko status na wayarka.
VIDEO: Yadda ake bude YouTube Channel
✅Abubuwan da zaka iya yiwa wayar koda bata kusa da kai 👇 👇
- Play sound- Hakan zai taimaka idan wayar na kusa zaka ji ƙara.
- Lost Mode- Hakan zai taimaka wajen kulle wayar ta yadda ba za'a iya amfani da ita ba.
- Erase iPhone- Hakan yana nufin goge duk wasu abubuwa da suke a cikin wayar, ta yanda ba za'a iya satar maka bayanai ko kuɗi ba.
MATAKI NA 3️⃣. Idan wayar an kashe ta ko ba'a amfani da ita a Internet
Yawanci mutane suna damuwa idan har wayar tana offline. Amma akwai abin da ya kamata ka sani:
- Google Find My Device zai nuna last seen location kafin a kashe wayar.
- Idan mutum ya haɗa ta da Internet daga baya, zata nuna location ɗin da take nan take.
- Masu iPhone kuma, Find My Network yana iya gano ta ko da ba a kunna ta ba, saboda Apple ecosystem yana amfani a kusa da iPhones.
VIDEO: Yadda Zaka gyara facebook Da aka kulle
MATAKI NA 4️⃣. Yadda zaka gano wayar ta hanyar IMEI
Idan ka rasa wayarka gaba ɗaya, zaka iya amfani da IMEI domin tracking. Ko wace waya na da IMEI (wasu lambobi guda 15)
Yadda zaka yi:
- Ka nemi IMEI a kwalin wayarka.
- Ko kuma idan kana da tsohon hoton dial #06#
- Sai ka kai report ga:
- Police
- Network providers (MTN, Airtel, Glo, 9mobile)
Wasu networks suna iya saka IMEI block ko su taimaka wajen gano inda ake amfani da SIM ɗinka.
VIDEO: Yadda zaka gyara Whatsapp da aka kulle
MATAKI NA 5️⃣. Tracking ta Banking Apps
Idan kana da apps kamar:
- Opay
- PalmPay
- Moniepoint
Waɗannan apps suna iya nuna maka inda aka yi login na ƙarshe ko device ID. Wannan bayani baya bada exact map na location, amma yana baka hujja idan kana son security investigation.
MATAKI NA 6️⃣. Yadda zaka kare kanka bayan wayarka ta ɓace
Ba wai tracking kaɗai ba, dole ka kare bayananka:
- Ka canza password na Gmail, Facebook, WhatsApp, TikTok.
- Ka cire active sessions daga sauran devices.
- Ka kulle ATM apps ɗinka.
- Ka yi block na SIM naka ta hanyar kiran customer care.
VIDEO: Yadda Zaka Gane Anyi Hacking Na Wayar ka
MATAKI NA KARSHE ✅. Me yasa wasu wayoyi basa tracking?
Dalilai:
- An kashe Wayar gaba ɗaya.
- An cire SIM.
- Ba ta da Internet.
- GPS ɗin wayar a kashe yake.
- Ba a haɗa wayar da Google/Apple account ba.
VIDEO: Yadda zaka canza PIN na Opay, Palmpay, Moniepoint
TAƘAITAWA (Summary)
Tracking na wayar da ta Ɓace ba abu mai wahala bane idan ka bi matakan da suka dace. Ko Android ko iPhone, akwai hanyoyi da dama da zaka gano location ɗinta, ko ka kulle ta, ko ka goge bayananka. Ka tuna security na wayarka yana farawa ne tun kafin ta ɓace. Ka tabbata kana da Google ko Apple account, sannan Ka kunna Find My Device tun kafin matsala ta faru.

0 Comments