YADDA ZAKA ƘWATO FACEBOOK ƊINKA DAGA WAJEN HACKERS – (How To Recover a Hacked Facebook Account)
GABATARWA (Introduction)
Facebook ya zama wani muhimmin bangare na rayuwar yau da kullum—ko kana kasuwanci, blogging, personal life, ko kuma social networking. Saboda haka, lokacin da hacker ya ƙwace maka Facebook account: za ka iya rasa abokai, kasuwanci, pages, ads account, ko ma bayanan sirri.
Yawanci mutane suna tunanin cewa idan an yi hacking, komai ya ƙare. Amma a zahirin gaskiya, akwai tabbatattun hanyoyin da da zaka bi ka ƙwato Facebook ɗinka cikin kariya. Wannan rubutu ya ƙunshi cikakken bayani dalla-dalla tun daga matakin farko har ƙarshe na yadda zaka ƙwato Facebook ɗin ka daga wajen Hackers.
VIDEO: Yadda Zaka Dawo da saƙon Whatsapp da aka goge
Kafin ka fara komai, kana bukatar ka tabbatar da cewa shin lallai an yi hacking ɗin?
⚠️Alamomin da ke nuna anyi Hacking na Facebook Facebook ɗin ka:
👉Za ka rinƙa ganin "Unknown login locations" daga ƙasashen da baka da alaƙa da su.
👉Zaka ga An canza password ba tare da saninka ba.
👉Zaka ga ba ka iya shiga account ɗinka duk da cewa password ɗinka daidai yake.
👉Zaka ga An canza recovery email ko phone number.
👉Zaka ga Hacker ya fara turawa mutane saƙonni daga shafinka (scam messages).
👉 Zaka ga Admin privileges a kan pages ɗinka sun bace.
VIDEO: Yadda Ake Tracking Na Wayar Da Ta Ɓace Ko Aka Sace
MATAKIN DA YA KAMATA KA ƊAUKA
Ka shiga wannan link → https://www.facebook.com/hacked
Ka Yi Amfani da “Secure Your Account” "Recovery System"
Facebook yana da tsarin gano hacking ta hanyar tambayoyi da verification.
HANYOYIN DA ZAKA BI
1. Ka shiga wannan Link ɗin facebook.com/hacked
2. Ka danna “My Account Was Compromised”
3. Ka shigar da email/phone da password na baya
4. Facebook zai tantance:
✅ IP address ɗinka
✅ Devices da kake amfani da su
✅ Old passwords
✅ Recovery options
5. Idan system ya tabbatar kai ne, za ka samu link na gyara password.
Note: Idan Facebook bai gane ka ba, ka yi retry bayan 1–2 hours saboda system yana refreshing.
Idan kuma Facebook ya gane kaine mai Account ɗin to zai baka damar shiga, to sai kabi waɗannan matakan:👇👇
1. Ka je **Settings & Privacy**
2. Ka danna **Security and Login**
3. Ka zabi **Change Password**
4. Ka yi amfani da strong password irinsu:
**HausaTech@2025Secure#**
5 Ka guji saka Password ɗin da kake amfani da shi a sauran apps.
Bayan ka gama Canza waɗannan abubuwan 👆👆👆👆to sai kayi ƙoƙarin Korar Hacker ɗin.
VIDEO: Yadda Ake Ƙwato Gmail Daga Wajen Hackers
MATAKAN DA ZAKA BI DOMIN KORARA HACKERS ƊIN
1. Ka shiga **Security and Login**
2. Ka duba sashen **Where You’re Logged In**
3. Za ka ga:
✅Devices
✅ Browser types
✅ Locations
4. Sai ka danna **“Log out of all sessions”**
5. Wannan zai rufe dukkan wuraren da hacker ya shiga ciki.
Bayan ka gama duka wadannan 👆👆👆👆 to sai ka ƙara wa Facebook ɗinka tsaro:
MATAKAN DA ZAKA ƘARAWA FACEBOOK ƊINKA TSARO
1. Ka je **Settings → Security and Login**
2. Ka danna **Two-Factor Authentication**
3. Ka zabi daya daga cikin wadannan:
* SMS code
✅ Authentication app (Google Authenticator)
* Security key
SHAWARA: Ka zaɓi Authentication App yafi tsaro.
VIDEO: Yadda Zaka Samu 1k YouTube Subscribers A Kullum
MATAKAN DA ZAKA BI:
1. Kaje >Play Store
2. Kayi download na "google Authentication"
3. Kayi register da Gmail ɗin ka
Ka Duba Recovery Contacts**
4. Sai ka koma **Settings → Security and Login**
5. Ka danna **Two-Factor Authentication** (zasu baka wasu code sai kayi copy ka dawo apps ɗin ka na Authenticator sai kayi paste)
6. Shike nan duk lokacin da kayi login out,idan zaka koma sai ka koma cikin apps na Authenticator ka ɗauko wasu code sai ka dawo wajen Facebook Login ka saka su sannan zai wuce.
👉Ka Duba Ko Hacker Ya Canza Email/Phone ɗinka:
Wasu hackers suna fara canza recovery info.
VIDEO: Yadda Zaka Canza PIN na Opay, Palmpay, Moniepoint
YADDA ZAKA DUBA:
1. Ka je **Settings → Personal Info**
2. Ka tabbata:
* Email naka ne
* Phone number naka ne
3. Idan ba haka ba:
❌ Ka goge wanda ba naka ba
✅ Ka saka naka daga farko
👉 Ka Duba Activity Log Domin Cire Abubuwan Da Aka Yi**
Hacker na iya:
* Canza page admins
* Tura spams
* Changing privacy settings
* Deleting posts
* Approving unknown logins
VIDEO: Yadda Ake Buɗe YouTube Channel
MATAKAN DA ZAKA BI
1. Ka je **Activity Log**
2. Ka duba:
* Story edits
* Page roles
* Post activities
3. Ka gyara duk abin da baka yi ba.
👉Ka Binciki App Permissions**
Wasu third-party apps suna bai wa hackers damar shiga Facebook.
MATAKAN DA ZAKA BI
1. Ka je **Settings → Apps and Websites**
2. Ka duba duk apps ɗin da ka bai wa permission
3. Ka cire duk wanda baka amfani da shi.
👉 Idan kuma Hacker Ya Karɓe Shafin Business Page**
Wannan yakan faru sosai—hacker ya cire ka daga admin!
VIDEO: Yadda Zaka gyara Facebook ɗin da Aka Kulle
MATAKAN DA ZAKA BI
1. Ka je **Business Manager → Security Center**
2. Ka yi request for page recovery
3. Ka nuna:
* Takardun shaida (ID)
* Old page admin proofs
4. Facebook yawanci na dawo da page idan ka nuna hujja.
👉Idan Baka samu damar Shiga Account ɗinka Gaba ɗaya ba**
❌Wannan shine worst-case scenario
MATAKAN DA ZAKA BI
Ka yi amfani da wannan:
https://www.facebook.com/help/contact/357439354283890
✅Wannan shine **official identity verification form**
Za ka bada:
* Passport/National ID/NIN slip
* Old email
* Screenshot na matsalar
Facebook yawanci na warware hakan cikin:
⏳ *24 hours – 7 days.*
VIDEO: Yadda Zaka gyara Whatsapp da aka Kulle
TAƘAITAWA (Summary)
A takaice, zaka iya ƙwato Facebook account ɗinka ta hanyar:
* Amfani da facebook.com/hacked
* Canza password
* Fitar da hacker daga devices
* Yin 2FA (authenticator app)
* Gyara email/phone
* Cire third-party apps
* Duba page admins
* Yin identity verification idan komai ya yi tsanani
Idan ka bi wadannan matakan gaba ɗaya, za ka ƙwato Facebook account ɗinka cikin aminci kuma ka hana hacking na gaba.

0 Comments