How to recover Gmail without phone number — Mataki-Mataki 2025📋
GABATAR WA (INTRODUCTION)
Mutane da yawa suna manta lambar wayar da aka sa a matsayin recovery ko kuma sun daina amfani da lambar number. Kada ku damu — Google na da hanyoyi da dama da za su taimaka maka ka dawo da account ɗinka, musamman idan kayi amfani da wayarka ko kwamfutar da ka saba amfani da ita.
A wannan rubutu zan nuna maku mataki-mataki —na yadda zaka dawo da Gmail dinka da sauran abubuwa kamar haka: Google Account Recovery page, recovery email, previous passwords, Recovery Contacts, da sauran abubuwan da za su taimaka.
VIDEO: Kada kayi watsi da wannan damar
Mataki na 1: Shiga shafin Google Account Recovery👇
accounts.google.com/signin/recovery
Wannan shine official only route da Google ya bayar don gyarawa.
👉Rubuta full Gmail address ɗin da kake son dawo da shi, sannan ka bi steps ɗin da za su biyo baya.
👉Mataki na 2: Yi amfani da Recovery Email ( recovery email shine email din wani abokin ka ko ɗan uwanka wanda ka saka a matsayin hanya ta biyu da Google zai iya tantance ka)
Idan ka taɓa saka recovery email a baya, Google zai iya tura OTP ko link zuwa wannan email ɗin — amfani da shi zai fi sauƙi fiye da waya.
Ka tabbata kana da ikon buɗe recovery email ɗin nan take. Idan ka canza ko ka rasa shi, yi kokarin shiga wani email ɗin da ka taɓa amfani da shi da account ɗin.
VIDEO: Sirrin da ba'a so kowa ya sani
👉Mataki na 3: Ka yi ƙoƙarin shigar da previous passwords
Google zai tambaye ka ka saka password na ƙarshe koda ba daidai bane (previous passwords) to a nan sai ka saka wani password wanda kake tunanin kamar shine— wannan na daya daga cikin manyan abubuwa da suke taimakawa wajen tabbatar da kai mai account ne.
Ka tuna duk kalmomin sirri da ka taɓa amfani da su, ma fiye da ɗaya idan za ka iya.
Mataki na 4: Kayi amfani da wayar da ka taɓa buɗewa da ita, idan kuma babu to sai kayi amfani da kowace waya.
Idan zaka yi recovery daga wayar da ka saba amfani da ita to akwai yuwuwar Gmail dinka ya dawo nan take, saboda Google zai ɗauka cewa wannan wurin yana da alaka da account ɗin.
Ka yi kokarin amfani da browser ko app da aka saba amfani da shi.
VIDEO: Kaɗan ne Daga cikin Mutane suka san wannan
Mataki na 5: Idan an yi hacking ko Disable account — to ga wata hanyar
Idan account ɗin ya kasance compromised wato (hacked) ko disabled, akwai dedicated recovery/help flows a Google Account Help.
Za ka ga options kamar “Secure a hacked account” ko “Recover a recently deleted account” — bi su a hankali kuma ka bayar da cikakken bayanin duk abubuwan da aka tambaye ka.
⚠️ABUBUWAN DA ZAKA YI BAYAN GMAIL DINKA YA DAWO (SAFETY TIPS)
👉Ka saita recovery email da recovery phone nan take.
👉Ka saka Enable 2-Factor Authentication (2FA) ko passkeys.
👉Saita Recovery Contacts (trusted friends).
👉Duba account activity (Recent devices & Security events) kuma ka canza password.
VIDEO: Abinda Maza keyi dani a Otal
TAƘAITA WA (SUMMARY)
Recovering Gmail without the registered phone is possible — Amma yana buƙatar amfani da official Google Account Recovery page, recovery email (idan akwai), previous passwords, familiar device/location, da sabbin options kamar Recovery Contacts.
Idan account ya kasance disabled ko hacked, sai abi steps na “Secure a hacked account” ko appeal forms.

0 Comments