How to Recover Deleted WhatsApp Messages?
GABATARWA (Introduction)
WhatsApp messages suna da matuƙar muhimmanci. Amma sau da yawa mutane kan goge saƙonni a bisa kuskure ko kuma wanda ya turo saƙon ya goge, ko kuma wayar su ta sami matsala. A wannan rubutu, za mu bi mataki-mataki na yadda zaka dawo da sakonnin WhatsApp da aka goge, ta hanyar amfani da Google Drive, Local Backup, da kuma iCloud ga masu iPhone.
VIDEO: Yadda Zaka Samu 1k YouTube Subscribers A Kullum
1️⃣ Fahimtar yadda WhatsApp ke ajiye bayanai
WhatsApp na yin backup ta hanyoyi biyu:
👉- Local backup (a cikin waya).
👉- Cloud backup (Google Drive ko iCloud).
Idan kana amfani da Android, WhatsApp zai ajiye bayanai ta Google Drive idan ka kunna backup. Amma idan kana amfani da iPhone, za a yi ta iCloud.
2️⃣ Yadda ake dawo da saƙonni daga Google Drive (Android)
VIDEO: Yadda Zaka Kulle ATM CARD da ya faɗi ko aka sace
👉- Ka tabbatar kana da backup a WhatsApp: ka shiga Settings >Chats >Chat Backup.
👉- Ka goge WhatsApp daga wayarka.
👉- Ka sake yin download daga Play Store.
👉- Bayan ka shigar, WhatsApp zai tambaye ka "Would you like to restore your chat history from Google Drive?
👉- Ka danna "Restore" , sai ka jira ya gama.
3️⃣ Idan babu Google Drive backup
VIDEO: Yadda Ake Buɗe YouTube Channel
Zaka iya amfani da Local backup.
👉- Ka shiga File Manager > WhatsApp > Databases.
👉- Za ka ga files masu suna "msgstore-YYYY-MM-DD.1.db.crypt14"
👉- Ka canza sunan yanda kake so, Misali: "Whatsapp Message"
👉- Ka sake shigar da WhatsApp kuma ka danna "Restore"
VIDEO: Yadda Zaka Gyara Facebook Disabled Account
4️⃣ Yadda ake dawo da saƙonni a iPhone (iCloud)
👉- Ka kunna iCloud Drive a Settings.
👉- Ka shiga WhatsApp >Chats >Chat Backup sai ka duba ranar ƙarshe da aka yi backup.
👉- Ka goge WhatsApp, ka sake download daga App Store.
👉- Bayan ka shigar, za a tambaye ka ka dawo da backup. Ka danna "Restore Chat History" .
5️⃣ Idan babu backup kwata-kwata
Idan baka kunna backup ba, babu hanya kai tsaye ta dawo da saƙonni. Amma zaka iya amfani da apps kamar Dr.Fone - WhatsApp Data Recovery, ko Tenorshare UltData. Amma sai ka kula da tsaron bayananka.
VIDEO: Yadda Zaka Gyara Whatsapp Da Aka Kulle
6️⃣. Shawarwari don gaba
👉- Ka dinga yin backup kowace rana ta atomatik.
👉- Ka tabbata kana da isasshen sarari a Google Drive/iCloud.
👉- Ka dinga Export chat masu muhimmanci lokaci-lokaci.
VIDEO: Yadda Zaka Gane Anyi Hacking Na Wayar ka
TAƘAITAWA (Summary)
Dawo da saƙon da aka goge a WhatsApp yana yiwuwa idan kana da backup. Idan ba ka da backup, zaka iya amfani da Local backup ko wasu recovery tools. Amma hanya mafi sauƙi ita ce ka tabbata WhatsApp ɗinka yana yin automatic backup akai-akai.

0 Comments