HOW TO BLOCK A LOST ATM CARD—MATAKI—MATAKI
GABATARWA (Introduction)
Rasa ATM card ɗinka da ke haɗe da fintech app kamar Opay, Palmpay, ko Moniepoint na iyajawo babbar Asara musamman idan akwai kuɗi a ciki.
A rubutun mu na yau zan nuna wasu hanyoyi da zaka bi domin kulle ATM ɗinka ta yanda ba za'a iya cire kuɗin dake ciki ba.
VIDEO: Sirrin Samun Kuɗi A YouTube
1. Me yasa ake bukatar kulle ATM?
Idan katin ka ya ɓace ko aka sace maka waya, mutum na iya:
👉- cire kuɗi a POS
👉- yin online shopping
👉- ko sayen data da airtime.
Kulle katin yana hana duk waɗan nan abubuwan faruwa.
2. Hanyoyin da zaka bi wajen kulle ATM card ɗin ka (Method 2025)
VIDEO: Sirrin Samun Kuɗi A FACEBOOK
👉MATAKI NA 1. Ta hanyar USSD code: zaɓi bankin da kake amfani dashi sai ka rubuta waɗannan lambobin
Wannan hanya ce mafi sauri idan baka da internet. Ga misalai daga bankuna da fintechs:
✅- Access Bank: *901*911#
✅- GTBank: *737*51*10#
✅- UBA: *919*10#
✅- First Bank: *894*911#
✅- Zenith Bank: *966*911#
✅- Opay: *955*131#
✅- Palmpay: *652# sannan ka bi umarni
✅- Moniepoint: *888# sannan ka zaɓi "Block Card"
VIDEO: Yadda Zaka Gyara Whatsapp Da Aka Kulle
👉MATAKI NA 2. Ta hanyar Mobile App
1. Shiga cikin bank app ɗinka (GTWorld, AccessMore, Palmpay, Opay, Moniepoint da sauransu).
2. Je zuwa Cards ko Manage Card.
3. Zaɓi >Block Card ko >Deactivate Card.
4. Ka cika umarnin da suka baka, sai ka ga sakon Card blocked successfully.
👉MATAKI NA 3. Ta hanyar SMS ko Email
Idan baka da internet, zaka iya aika saƙo zuwa email ɗin bankinka.
Misali: Example Message (English):
Subject: Block my ATM card
Message:
Hello,
Please block my debit card linked to account number (123456789 ka cire wannan lambobin sai ka saka lambar account ɗin ka)
The card has been lost and should be deactivated immediately.
Thank you.
VIDEO: Abin Mamaki: Yadda Zaka Gane Anyi Hacking Na Wayar Ka
👉MATAKI NA 4. Ta hanyar ziyartar banki
Idan baka da damar amfani da waya, ka iya zuwa bankinka kai tsaye tare da ID card don su kulle katin daga tsarin su.
Bayan ka kulle ATM card ɗinka
- Ka tabbatar ka karɓi sabon katin daga banki cikin kwanaki 5.
- Ka duba transaction history don tabbatar babu wanda yayi amfani da shi.
- Ka sabunta PIN ɗinka idan kana zargin wani ya sani.
VIDEO: Yadda Zaka Dawo Da Gmail Ɗin Ka Ba Tare Da Lambar Waya Ba
TAƘAITAWA (Summary)
Rasa ATM card ɗinka ko fintech card ba ƙaramin abu ba ne, amma da matakai kaɗan zaka iya kare kuɗin ka gaba ɗaya. Ko ta USSD, App, ko Email zaka iya kulle katin nan take. Ka tuna: Kullewa cikin lokaci zai kare ka daga asararkuɗi!

0 Comments