How to Open a YouTube Channel—Mataki-mataki
GABATARWA (Introduction)
Bude YouTube Channel yanzu hanya ce mai sauƙi wacce take ɗaya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗaɗe, ta hanyar wallafa bidiyo, sadar da ilimi, ko fara kasuwanci.
A Wannan rubutu zamu bayyana matakai na bude channel, yadda za ka saita shi, da yadda zaka fara tura bidiyoyi masu kayatarwa, har zuwa yadda zaka fara samun kuɗi dashi.
VIDEO: Yadda Zaka gyara Whatsapp da aka kulle
1️⃣ Abubuwan da zaka tanada kafin ka buɗe YouTube Channel.
Kafin ka fara, akwai abubuwan da ya kamata ka tanada:
- 👉Gmail account wanda zaka rinƙa amsar saƙonni.
- 👉Smartphone ko laptop.
- 👉Kyakkyawan suna mai sauƙi wanda za a iya karantawa.
- 👉Nau'in content da kake son yi: Misali: Nishaɗi, Koyarwa, Tech, Cooking, Hausa News, Comedy, Review, Lifestyle ko Vlog.
2️⃣. Matakan BuÉ—e YouTube Channel
✅A. Create Gmail Account
- 👉Shiga wannan Link ɗin www.gmail.com
- 👉Danna >Create account
-👉 Cika bayananka sannan ka tabbatar ka ajiye password inda bazaka manta ba.
VIDEO: Yadda zaka gane an yi Hacking na wayar ka
✅B. Buɗe Channel
-👉 Shiga YouTube ka shiga da Gmail ɗin da ka buɗe.
- 👉Danna profile icon a sama.
- 👉Zaɓi >Create a Channel.
- 👉Saka sunan da kake so.
- 👉Confirm. Nan take za ka samu sabon channel ɗin ka.
3. Saita Channel ɗiin ka Domin ta yadda zai rinƙa fitowa a YouTube da Google
✅Domin ka sa channel ɗinka ya zama professional:
- 👉Saka profile picture mai kyau (kamar logo).
- 👉Ƙirƙiri banner mai girman Pixel 2048—1152.
- 👉Rubuta manufar ka da abubuwan da kake wallafa wa da manufar ka (channel description).
- 👉 Saka links na sauran shafukan ka, kamar Facebook, Instagram ko website.
VIDEO: Yadda Zaka Canza PIN na Opay/Palmpay/Moniepoint
4. Yadda Ake Uploading Bidiyo
- 👉Danna > create ko Upload video.
- 👉Zaɓi bidiyon da kake so ka ɗora.
- 👉Rubuta title mai jan hankali. Misali: "Yadda Zaka Samu 1k YouTube Subscribers A Sati Ɗaya"
- 👉 Rubuta guntun bayani na abinda bidiyon ya kunsa.
-👉 Saka tags (keywords) domin YouTube ya fahimci content ɗinka.
- 👉Zaɓi thumbnail mai kayatarwa da zai jawo hankalin yan kallo.
5. Shawarwari Don Samun Nasara a YouTube
- 👉Ka kasance consistent ka rinƙa yin bidiyo 2-4 a mako.
-👉 Ka yi amfani da thumbnail da titles masu jan hankali.
- 👉Ka inganta murya da haske a bidiyoyinka.
-👉 Ka rinƙa reply a comments domin gina community.
- 👉Kada ka kwafi bidiyon wasu domin guje wa YouTube strike.
-👉 Ka yi amfani da keywords yayin rubuta title da description.
VIDEO: Yadda Zaka Dawo Da Gmail Ɗin Ka Ba Tare Da Lambar Waya Ba
TAƘAITA WA (Summary)
Wannan rubutu ya nuna duk abubuwan da ake buƙata wajen buɗe YouTube channel, daga, budewa, saitawa da fara ɗora bidiyo.
Hakanan akwai shawarwari da zasu taimaka maka wajen samun nasara da wuri, musamman idan kai sabo ne a YouTube. Bi matakan nan ka fara tashi cikin sauƙi
VIDEO: Yadda Zaka Cire Virus Daga Wayar Ka

0 Comments