ABIN MAMAKI: YADDA ZAKA GYARA FACEBOOK DISABLE ACCOUNT

  


How to Recover a Disabled Facebook Account— Cikakken bayani 


 GABATARWA (Introduction)

A lokuta da dama, mutane kan samu matsalar Facebook ya dakatar da account ɗin su (Disable)— ba tare da gargadi ba.

 Wannan na iya kawo cikas ga kasuwanci, sadarwa, harkokin yau da kullum, ko kuma shigar da bayanai. A wannan rubutun zan yi cikakken bayani wanda ya tattara duk abin da ya kamata ka sani—daga dalilan da ke kawo disabling, zuwa yadda zaka yi appeal, har zuwa yadda zaka kare kanka, domin kada matsalar ta sake Faruwa. 

VIDEO: Yadda Zaka Gane anyi Hacking Na Wayar Ka da Kuma Yadda Zaka Gyara

YADDA ZAKA GYARA MATSALAR FACEBOOK DISABLE ACCOUNT 

1. Dalilan Da Ke Sa Facebook su kulle maka Account (Disable)

Facebook ba ya kulle account haka kawai; sai da wasu dalilai kamar haka:👇

👉 Keta dokokin Community Standards, musamman abubuwan da suka shafi tsiraici, tashin hankali, ko kalaman kiyayya.

👉Aika saƙonnin spam, ko amfani da bots na aikawa da requests da yawa cikin kankanin lokaci.

👉Aika friend requests ga mutane da yawa ba tare da sanin su ba.

👉An yi repeated reports daga wasu users.

👉Login daga sabuwar na'ura ko wuri wanda Facebook ya ga bai dace da al'adar amfanin ka ba.

👉Yin amfani da sunan karya ko identity mara inganci.

VIDEO: Yadda Zaka Canza PIN a Opay/Palmpay/Moniepoint

2. Abin Da Ya Kamata Ka Fara Yi Kafin Ka Nemi a Dawo Maka Da Account

Domin ka yi successful appeal, ya kamata ka tabbatar kana da:

1️⃣ Email ko lambar wayar da ka buɗe asusunka.

2️⃣ Hoton ID mai inganci (National ID, Driver License, PVC, ko International Passport).

3️⃣ Sunan da ka saka a Facebook, kamar yadda yake, ba tare da canji ba.

4️⃣ Bayanin ƙarshe na lokacin da ka yi amfani da account ɗin.

VIDEO: Yadda Zaka Dawo Da Gmail Ba Tare Da Lambar Waya Ba

3. Hanyoyin Da Zaka Bi Domin Dawo Da Disable Account (Mataki-mataki)

A. Appeal Form

- Jeka kai tsaye zuwa wannan Link ɗin 

https://www.facebook.com/help/103873106370583?utm

- Cika full name ɗinka daidai kamar yadda yake a profile.

- Saka email ko number da ke haɗe da asusun.

- Saka clear picture na ID ɗinka.

- Rubuta gajeren bayanin da ke nuna cewa baka karya dokar Facebook ba, ko cewa an yi kuskure.

- Aika form ɗin ka jira response (yana iya ɗaukar awanni 24 zuwa kwanaki 7).

VIDEO: Yadda Zaka Cire Virus A Cikin Wayar Ka

B. Identity Verification

Idan Facebook ya bukaci ka tabbatar da kai ne mai account:

- Za su aiko maka da link don ka loda hoton fuska.

- Ka tabbata hoton ya kasance a fili kuma haske bai ɓata fuskar ka ba.

- Idan sun yi matching da ID ɗinka, za su buɗe account ɗinka.


C. Idan Har Ka Shiga Amma Ka Ga Warning

- Canza password nan da nan.

- Cire duk apps marasa tushe.

- Kunna Two-Factor Authentication.

- Duba ko akwai devices da ba ka san su ba sai ka cire su.

YANZU YANZU: Najeriya Zata Ɗauki Sabbin Ma'aikata

4. Abubuwan Da Ya Kamata Ka Guje mawa Bayan An Dawo Maka Da Account

- Kada ka sake yin spam ko overly aggressive adding.

- Ka guji amfani da abubuwan da ba official ba (unauthorized apps).

- Ka rage yawan wallafa posts masu tashin hankali ko rigima.

- Ka tabbatar komai da kake rubutawa na bin ƙaidojin Facebook.

VIDEO: Kada ka Kalli wannan Bidiyon

TAƘAITA WA (Summary)

Wannan post ya bayyana dalilan da ke sa Facebook ya kulle account, abubuwan da ya kamata ka shirya, da matakai guda uku na dawo da account: appeal form, identity verification, da security checkup. Hakanan ya ƙunshi shawarwari masu muhimmanci domin kiyaye account ɗinka daga sake samun matsala a gaba.

Post a Comment

0 Comments