![]() |
| Matashi kuma ɗan kasuwa yana amfani da AI wajen rubuta talla a online |
“Yadda Artificial Intelligence (AI) Ke Sauya Hanyar Tallace-Tallace da Kasuwanci”
Fasahar AI ta zama sabon makamin ‘yan kasuwa wajen samun kwastomomi da ƙara riba cikin sauƙi.
Gabatarwa:
Yau kasuwanci ya koma kan wayar hannu Idan baka iya tallata kaya a Facebook, Instagram, ko WhatsApp ba — kana barin kuɗi a teburin wasu.
Amma da zuwan AI, yanzu zaka iya yin tallan da ke jawo hankalin mutane, da ban sha'awa, cikin sauƙi!
VIDEO: Jerin Sabbin Jihohin Da Gwamnatin Najeriya Ta Samar
1️⃣ Ka Fara da Hoton da ke Jan Hankali
Mutane basu cika karanta post na rubutu ba— sunfi son kallon hoto 👀.
Ka tabbata hotonka yana da kyau, haske, kuma yana nuna kayan da kake so ka tallata.
🧩 Misali: Idan kana siyar da takalma: to ka tsara hoton mutum ya saka takalmin a kafar sa hakan zai ba wani sha'awa har ya siya.
Idan abincin kaji ne: to ka saka hoto lafiyayyun kaji suna cin abincin naka.
💡 AI Tool: Canva Magic Studio, Leonardo.ai, ko ChatGPT + DALL·E suna iya taimaka maka ƙirƙirar irin waɗannan hotuna a cikin mintuna kaɗan.
VIDEO: Abin Mamaki Yadda Zaka Gano Wayar Ka Data Bace A Duk Fadin Duniya
2️⃣ Rubuta Jimla Ta Farko Mai Jan Hankali (Hook Line)
Rubutun farko shine yake jawo hankalin mai karatu.
Ya zama gajere, mai daɗin karantawa, kuma mai ban sha’awa.
🧩 Misalan Hook Lines da zaka iya amfani da su:
1. “Ka tsaya minti ɗaya — wannan takalmin ba kamar sauran ba ne!”
2. “Kana neman abincin da zai sa kajinka su ƙara lafiya cikin sati ɗaya? Ga mafita!”
3. “Flask ɗin da ke riƙe zafi har awanni 24? Haka ne — gaskiya!”
4 “Kyauta ce ta musamman ga mai kaunarka, amma har yaushe?”
5. “Kar ka bari wannan damar ta wuce ka — rangwame zai ƙare da yamma!”
VIDEO: Fasahar Da Zata Canza Maka Rayuwa Mai Dadi
3️⃣ Ka Nuna Amfanin kaya da ƙarkon su,
Masu siye suna son sanin me yasa wannan kayan yake da amfani gare su, ba kawai menene shi ba.
🧩 Misali: Kada ka rubuta: “Muna da sabbin takalma masu kyau.”
✅ Ka rubuta: “Takalma masu taushi da ƙyalli — ba sa zafi ko da ka yi tafiya mai nisa.”
VIDEO: Wani Sirri Da Ba'a So Kowa Ya Sani
4️⃣ Ka nuna wa Mutane Wurin Da Zasu Shiga Domin Siyan Kayan ka (Call To Action - CTA)
Kada ka bar post ɗinka haka kawai. Ka gaya musu abin da kake so su yi bayan karantawa.
🧩 Misalan CTA:
1. “Tura mana sako yanzu ka sami rangwame 20%!”
2. “Danna wannan link domin ganin sabbin kayayyaki.”
3.“Kada ka bari a baka labari, latsa nan domin samun rangwame.
5️⃣ Ka Yi Amfani da AI don Inganta Tallar ka.
AI tana iya baka jimloli da rubuce-rubuce masu jan hankali cikin kankanin lokaci!
Misalan apps da zasu taimaka maka:
🧩 ChatGPT: don rubuta tallace-tallace da captions.
🧩 Copy.ai: don ƙirƙirar rubutun talla masu jawo hankali.
🧩 Canva Magic Write: don haɗa hoto da rubutu kai tsaye.
Kammalawa:
A yau, tallan da yafi tasiri a social media shine wanda yake:
1. Gajere,
2. Mai hoton da ke jawo hankali,
3. Da kalmomi masu motsa zuciya.
AI na baka wannan dama — ka faɗa mata abin da kake siyarwa, sai ta baka rubutun da ya dace da kasuwancinka.

0 Comments