ABIN MAMAKI: Yadda Zaka Bibiyi Wayar Ka Da Aka Sace Ko Ta Ɓace

 




Yadda Za Ka Bibiyi Wayarka da Ta Ɓace Ta Hanyar Amfani da Lambar IMEI

🧭 Ka gano yadda za ka nemo wayarka da ta ɓace cikin sauƙi


Gabatarwa:

Rasa waya na iya zama abin damuwa matuƙa, musamman idan tana ɗauke da bayanai masu muhimmanci, hotuna, ko saƙonnin da suka shafi rayuwa.

 Amma akwai kyakkyawan labari! Za ka iya bin sawun wayarka ta amfani da lambar IMEI.

Lambar IMEI wata lamba ce mai ɗauke da haruffa 15 da ake bai wa kowace waya a duniya, domin gane ta musamman ko da an canza SIM.

       Idan har ka san yadda zaka yi amfani da lambar IMEI, to zaka iya samun taimako wajen gano wayarka da ta ɓace cikin sauri.

VIDEO: Yadda Ake Gane Mace Mai Neman Maza

Menene IMEI?

IMEI na nufin International Mobile Equipment Identity — wato wata lamba ce ta musamman da ke bayyana kowace waya a duniya. 

Wannan lambar tana taimakawa wajen gano ko toshe waya idan aka sace ta ko aka yi amfani da ita ta hanyar da ba ta dace ba.


Yadda Za Ka Samu Lambar IMEI ɗin Wayarka


Idan baka rubuta IMEI ɗin ka ba kafin wayarka ta ɓace, akwai hanyoyi da zaka iya amfani da su don gano ta:

Hanya ta 1: Shigar da Code

Ka buɗe dialer a wayarka ka rubuta:

*#06# sai ka danna Send/ok/call

Nan take lambr IMEI zata bayyana 


🟢 Hanya ta 2: Jeka cikin Setting na Wayar Ka 

Android: Settings → About Phone → Status → IMEI


iPhone: Settings → General → About → IMEI


VIDEO: Banbancin Mace Mai Ƙiba da Siririya Wajen Kwanciya


🟢 Hanya ta 3: Ka duba Kwalin wayar ka ko Takardar Siyan Waya


Duba Kwalin wayar ka ko rasidin siye, yawanci ana rubuta IMEI a jikin sticker.


🟢 Hanya ta 4: Je ka zuwa Google Account (Android)


Ziyarci https://www.google.com/settings


Shiga account ɗinka → Find your phone → Zaɓi wayar → Duba IMEI.


🟢 Hanya ta 5: Ta Apple ID (iPhone)


Shiga appleid.apple.com

 → Sign in → Devices → Zaɓi iPhone ɗinka → Duba IMEI.



Post a Comment

0 Comments