![]() |
| “Sabon mutum-mutumin Bumi daga China — yana rawa, tafiya, da koyarwa cikin farashi mai sauƙi.” |
Kamfanin Noetix Robotics daga Beijing (China) ya ƙera sabon mutum-mutumi mai kama da ɗan adam wanda ake kira Bumi.
Wannan mutum-mutumin ba shi da tsada kamar na kamfanin Tesla Optimus, domin farashinsa bai wuce naira miliyan ɗaya da ɗan abu (kimanin $1,400).
Bumi ba wani babban mutum-mutumi bane — yana kama da ƙaramin yaro saboda tsayinsa kusan kafa uku ne, nauyinsa kuma kusan kilo 12.
Ana iya sa shi:
1. Yana tafiya,
2. Yana rawa,
3. Kuma yana taimakawa wajen koyar da yara ko dalibai.
Masana kamfanin sun ce nan gaba mutum-mutumin zai iya koyon wasu ayyuka kamar koyarwa da kera abubuwa, ta hanyar shirin (programming).
Hakan yana nufin matasa masu sha’awar fasaha da robotics za su iya koyon amfani da irin wannan mutum-mutumi a gida ko makaranta.
Za a fara siyar da Bumi ta hanyar pre-order (aijewa tun kafin fitowa) daga ƙarshen wannan shekara.
Duk da cewa ba za ka iya amfani da shi a masana’anta ko wajen ɗaga kaya masu nauyi ba, amma farashinsa ya fi sauƙi sosai idan aka kwatanta da sauran mutum-mutumi masu kama da mutum kamar Tesla Optimus wanda farashinsa ya kai daga $5,900 zuwa $20,000.

0 Comments